Bene Mai hawa 3 ya rushe a Port Harcourt
Wani Gini mai hawa uku ya rushe akan hanyar Popular Bende a Tsohuwar hanyar cikin gari ta Port Harcourt a Jahar Rivers.
A cewar wanda ya shaida lamarin, ginin wanda aka gina shekaru aru-aru da suka gabata, ya rushe ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 2 na dare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ko kaɗan Rasha ba zata razana kan Haɗin Gwuiwar Sojoji na Amurka a Europe — Inji Mataimakin Ministan Ƙasashen Waje
“Ginin na ɗaya daga cikin tsofaffin gine-gine a Port Harcourt da ake kira da Ginin Fararen Fata. Nayi imanin cewa yana ɗaya daga cikin gine-ginen da aka kyale a Port Harcourt bayan faɗan farar hula. Ya rushe da misalin ƙarfe 2 na dare a ranar Laraba, amma ba’a rasa rai ba. Babu kowa cikin ginin ya zuwa lokacin da ya rushe” Inji wani daya shaida lamarin
A lokacin da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan Sandan Jahar Rivers Iringe Grace Koko yace babu kowa a ginin a lokacin da ya rushe.