By Ishaq Dabai
Jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kama wanda ake zargi na biyu a matsayin kwamanda kuma magajin sarkin yakin na jihar Benue, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana, Kefas Aondofa wanda ake kira Azonto.
Wata majiyar soji data nemi a sakaya sunanta ta shaida wa manema labarai a babban birnin jihar Benue, cewa jami’an tsaro sun cafke Azonto a jihar Taraba ranar Alhamis da ta gabata bayan wani aikin hadin gwiwa da suka gudanar a yankin.
Majiyar ta yi bayanin cewa Azonto da mambobin sa sun dade suna addabar kauyukan karamar hukumar Ukum da wasu sassan jihar har zuwa lokacin da aka cafke shi.
Majiyar tace: ‘’ A gaskiya, an yi kamen ne a Taraba ba a nan Binuwai ba amma kun san yana cikin jerin wadanda muke kallo. daya dade yana addabar al’ummomin da ke kusa da yankin Ukum.
“Tare da kokarin sojojin mu da na DSS mukayi hadin gwiwa, mun sake samun nasara a yakin da muke da ‘yan fashi da masu aikata laifuka.”
Ya kara da cewa tattara bayanan sirri da aka yi tsakanin hukumomin tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya ya haifar da kame shugaban ‘yan bindigar a maboyarsa, ya kara da cewa yana sanyaya sawu a hannun DSS.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa sojoji sun kashe Gana sama da shekara guda da ta wuce yayin da yake kan hanyar sa ta zuwa gidan Gwamnati dake Makurdi don yin afuwa ta biyu amma hakan bai nuna karshen ayyukan da mukaddashinsa ke yi a jihar dama sauran unguwanni ba.