Karim Benzema na iya rasa wasan da Real Madrid da kara da Atalanta a gasar zakarun Turai a mako mai zuwa, bayan da Zinedine Zidane ya tabbatar da cewa dan wasan ya ji rauni yayin wasa ranar Alhamis.
Benzema bai halarci atisaye a safiyar yau Juma’a ba, kuma Zidane ya ce, bai cikin tawagar ‘yan wasan da zasuyi tattaki ranar Asabar domin karawa da Real Valladolid a gasar Laliga.
To sai dai, Har yanzu kungiyar ba ta tabbatar da takamaiman irin rauni da dan wasan ya samu ba.