Wata kyakkyawar mata mai shekara 57 a duniya, ta auri abin ƙaunarta tana sanye da wata rigar amare mai launin ja.
Matar ta sanya wani ɗan gajeran bidiyo a TikTok, wanda ya nuna lokacin da ta iso wajen taron bikin. Bidiyon da yanzu haka sama da mutum miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu suka kalla. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Mahafinta mai shekara 80 a duniya shine ya rakota zuwa wajen bikin. Dattijon sam bai yi kama da shekarun sa, inda kamanninsa suke kamar na wani mai sauran jini a jika.
KU KARANTA KUMA: Wasu abubuwa 2 da dole sai Arsenal tayi su kafin ta samu nasarar lashe Premier
Alamu suna nuna cewa matar tayo gadon kyau ne daga wajen mahaifinta, domin a 57 wasu mutane da dama sun kasa yarda cewa shekarunta kenan. Saboda tayi kama da wacce bata kai hakan ba.
Da ita da mahaifinta sun taho suna tafiya kamar wasu sojoji zuwa cikin wurin bikin, cikin da ƙasaita da farin ciki.
Abinda yafi ɗaukar hankali shine yanayin yadda ta tashi daga al’adar amare ta sanya fararen kaya a wajen biki zuwa jajayen kaya.
Wani mai amfani da @blondlocs, shine ya sanya bidiyon a manhajar TikTok.
Ku kalli bidiyon a nan
Idan Ina Sallah Tunaninta Nake Yi Amma Ta Guje Ni -Matashi Ya Koka
A wani labarin na daban kuma wani matashi ya koka bayan budurwarsa da yake matuƙar so ta guje shi.
Matashin wanda ya bayyana cewa yana matuƙar son budurwar tasa, yace bai yi wa budurwar tasa laifin komai ba amma ta saka masa da wannan cin amanar.
Matashin a cikin takarda da ya aikowa shafin Northern Hibiscus a manhajar Facebook, ya bayyana irin tsantsar son da yake yiwa budurwar tasa.