Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fito fili ya yi magana kan bidiyon badakalar chusa dala a aljihu.
Idan za’a iya tunawa dai a shekara ta 218 ne wata jarida mai suna Daily Nigeria wacce ke aiki a yanar gizo ta fitar da wasu faya-fayan bidiyo dake nuna Ganduje na damkar dalaloli hannun wani dan kwangila.
Wadanchan Bidiyo sun janyo cece-kuce tsakanin jama’a inda har ya kai ga Majalisar dokokin Jihar Kano ta kafa wani Kwamiti don binciken gaskiyar lamarin bidiyon.
To sai dai bayan bullar bidiyon Ganduje bai ce uffan ba sai kwatsam aka ji shi cikin wani shirin Tashar Rediyon BBC Hausa Mai suna “A Fada A Cika” wacce ta gabatar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Maganar ta Ganduje kan badakalar ta biyo bayan tambaya ce da wani dan Kano mai suna Kabiru Sa’idu Dakata ya yi kan irin matakan yaki da rashawa da Ganduje ke dauka.
Ganduje ya ce tabbas wadanchan bidiyo soki-burutsu ne kawai, to amma ya ce har yanzu ana ci gaba da gundanar da bincike kan lamarin.
“Tilas mu hukunta duk wanda ke da hannun gurin yada wadanchan bidiyo wanda an yi ne don taba kimar mu, babu shakka dukkanin su soki burutsu ne kawai kuma muna nan muna gabatar da binciken sirrin kan hakan, kuma duk wanda ke da hannu to lallai sai mun bashi kunya” A cewar Ganduje.
Ya kara da cewa “Babu gaskiya a bidyion kuma babu wani abu mai kama da haka da ya faru, an yi ne kawai don hana ni sake tsayawa takara kuma na tsaya din, sun yi ne don hana zarcewa kuma naq zarce. Amma dai hakan ba wani babban al’amari ba ne, babban lamari a nan shine dole ne mu hukunta ko waye dake da hannu”
Ganduje ya kuma tabo wasu bangarorin matsaloli da suka shafi jihar Kano wadanda suka kunshi sayar da filaye da kasuwar kayayyakin sawa na Kantin KWari da batun titunan sama na flyovers da kuma wasu ayyuka da gwamnatin sa ke kokarin aiwatarwa.