Wani bidiyo ya nuna wani mataki yayin da ya kira waya yana ta hayagaga inda yake bayyana cewa budurwarsa ta yi masa sata, LIB ta ruwaito.
A cewarsa, ba su wuci mako biyu tare ba, amma ta sace duk wasu tsadaddun kayan da ke dakinsa musamman sutturu.
An bidiyon ana kyauta zaton budurwar tasa ya kira yana sauke wa takaicinsa inda yake tambayarta idan ta san tsadar kayan da ta sace.
Tabbas a bidiyon idan mutum ya kula, matashin a dugunzume yake kuma watakil ko gidan iyayenta bai sani ba.
Soyayyar makonni biyu ba lallai bane namiji ya kai ga sanin gidan iyayen budurwarsa ba. Tirkashi! Sai dai muce Allah yasa a wanye lafiya. Don tabbas idan su ka hadu, a yadda yake fadan nan, ta wuya ya bar ta.
Ga bidiyon a kasa:
Yadda Wata Zabgegiyar Budurwa tayi kukan kura ta faɗa cikin Teku bayan amsa wata waya
Wata yarinya da har yanzu ba a tantance ba ta kashe kanta ta hanyar tsalle daga gadar Gbodofon zuwa cikin kogin Osun a ranar Alhamis a Osogbo.
A cewar shaidun gani da ido, matashiyar ta faɗa cikin Kogin bayan da aka buga mata waya da misalin karfe 4:00 na yamma.
A cewarsu, yarinyar ta hawo Babura zuwa gadar da ke kan hanyar Gbongan zuwa Osogbo.
Wani ganau mai suna Tosin Olaleye ya shaidawa DAILY POST cewa matar tana tattaunawa da wani a waya lokacin da ta isa gadar.