Bifra: Samun Takarar Peter Obi ya taƙaita ta’addancin IPOB — Gumi
Malamin Addinin Musulunci a Najeriya Ahmad Gumi yace samun Takarar Peter Obi a matsayin Ɗan Takarar Shugaban a Jam’iyyar PDP a Shekarar 2023 ya sanya an samu sauƙin zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook, Malamin yace Ƙungiyar Tsàgerun Biafra, IPOB sun goyi bayan Obi, shiya Sanya neman raba ƙasar siyasa ce.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tinubu-Shettima: Yanzu APC ta zama ta Ƴan Ta’adda — HURIWA
Da yake bayyana irin matsalolin tsaro a ƙasa da rashin sanya kowa a dama dashi, yace aikace-aikacen Oduduwa yayi ƙasa biyo bayan samun Takarar Tinubu a matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC.
Sanarwar tace “dukkanin nema ƴanci da raba kasa ya ragu bayan Peter Obi ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party. A garesu Inyamurai suna da Jam’iyya. Wannan ya nuna cewa dukkanin abubuwan su, siyasa ce.
“Neman kafa Kasar Oduduwa shima ya tsaya cak, bayan Tinubu ya samu Tikitin Takarar APC, Kuma hakan bazai taɓa dawo wa sai dai in bai samu cin zaɓe ba.
A cewar sa Babbar Matsalar Ƙasar nan shine ko INEC zata gudanar da Sahihin Zaben