Awannan rana ta Talata za ayi bikin buɗe sabuwar gasa mai taken Honarable Bala Dawaki Tarauni Sports Competition a ƙaramar hukumar Tarauni wanda aka sanya, saidai tun jiya akaso ayi bikin buɗe gasar amma hakan bai yiwwuba sakamakon wasu dalilai.
Amma a yau 22 ga watan Satumba 20202 za ayi bikin buɗe wannan gasa inda za a fafata wasan farko tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta F/c Unguwa Uku da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta F/C Ajax Dawakin Kudu inda za a fara wasan da misalin ƙarfe 3:45.
Haka awannan gasa dai an bayyana cewa mai girma ɗan majalissar tarayya dake wakiltar Dawakin Kudu da Warawa wato Hon. Mustapha Bala Dawaki wato mai gidan ruwa shine babban baƙo kuma a gabansa za ayi bikin buɗe wannan gasa.
Shidai wannan ɗan majalissar yana baiwa kowanne ɓangare haƙƙinsa wajen yin abin da ya kamata tunda kusan duk a faɗin jahar Kano ana yabawa yadda yake baiwa harkar wasanni gudun mawa tunda matasa ne da yawa acikinta kuma shi mutum ne na mutane.