Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu mutane 128 da take zargin ‘yan daba ne a yayin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-El-Fitr a fadin masarautun jihar biyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Kano.
Ya ce kamen ya yi daidai da umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar na samar da isasshen tsaro a lokacin bukukuwan Sallah.
A cewarsa, an kama mutane 128 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin bikin “ sallar Eid karama” da “Hawan Daushe” da “Hawan Nassarawa” da “Hawan Fanisau” a dukkanin masarautun jihar biyar dake fadin jihar.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da muggan makamai, da kwayoyi masu sa maye, da kuma zargin laifukan sace-sace.
Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya godewa gwamnati da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Kiyawa ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala gudanar da bincike.
A wani labarin Kuma na daban.
Barau Ya Janye Kudurinsa Na Tsayawa Takarar Gwamna, Ya Sayi Fom Din Sanata Dan Fafatawa Da Ganduje
Shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin na Kano ta Arewa ya janye kudirinsa na tsayawa takarar gwamna tare da sayen fom din takarar Sanata.
Da wannan ci gaba Barau zai kalubalanci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda masu ruwa da tsakin jam’iyyar suka amince masa da ya nemi wannan kujera.
Barau, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar gwamna a jihar Kano, ya janye aniyarsa ta sa’o’i 24 bayan Ganduje ya nada mataimakinsa a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar.
Majiyoyi sun ce dan majalisar wanda daya ne daga cikin shugabannin kungiyar G-7 da ta balle a jam’iyyar APC ta Kano, shugabannin jam’iyyar sun yi nasara a kan ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna ya koma majalisar dattawa.
Dan majalisar, a wata hira ta wayar tarho ya tabbatar da cewa ya dauki fom din komawa kungiyar ta Red Chamber.
Idan za iya tunawa a jiyane masu ruwa da tsakai suka baiwa gwamnan kano Abdullahi Ganduje damar tsayawa takarar Sanatan kano ta Arewa.
Sai dai a iya cewa wannan matakin da gwamnan kano ya samu baiyiwa Barau Jibrin dadi ba inda ya yanke shawarar a jiye ta karar sa ta gwamna ya nemi fom din karar sanata.