Gwamnatin Jahar Sokoto ta rabawa Masarautu 87 dake Jahar zunzurutun kudade kimanin miliyan 21.7 don sayama marayu dake karkashin Masarautun naman Sallah. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Kowane Masarauta ta karbi dubu dari biyu, da kuma kudin daukan shanun zuwa kowace Masarauta dubu ashirin.
Sarkin Musulmin dake Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar Sa’id, ya jinjinawa gwamnatin Jahar Sokoto kan irin wannan babbar hidima duk da yanayin tattalin arziqin kasar yayi kasa.
KARANTA:- TIRKASHI: An sallami Shugaban makarantar Sakandire a Kano kan barin yara zuwa hutun Sallah
Kamar yadda yace, wannan zai sanya marayun jin cewa ba a barsu a baya ba.
Sarkin Musulmai Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar Sa’id, yayi gargadi ga Masarautun da suyi adalci wajan tabbatar da kowa ya gudanar da abun aka umarce shi.
Yace “Ina kira da kowane Masarauta kada tayi amfani da kudaden da aka tura musu wajan biyan bukatun kansu, idan bazaka iya karawa ba to kada ka rage akan abunda aka baka.”
Tun farko dai Malam Muhammad Maidoki shugaban Hukumar dake kula da Zakkah na Jahar Sokoto, ya umarci Sarakunan don fara aikin da aka dora musu.
A wani labarin
Wani Minista ya sanyawa Limamai sharuda a lokacin babbar Sallah
Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammed Musa Bello, ya gindaya sharudda ga Limamai a lokacin gudanar da Sallah domin takaita yaduwar cutar Covid-19 karo na uku.
Wannan sanarwar ta fito ta hannun Sakataren sa Anthony Ogunleye.
Ministan ya sanya doka wajan gabatar da huduba kada tayi tsawo, sannan a kammala komi da komi a cikin awa daya.
Ya kara da cewa wajan gudanar da Sallah ya kasance an raba adadin masu shiga kashi biyu don samun tazara.
A yayin gabatar da bukukuwan Sallah a garin Abuja, yace duk wani gidan motsa jiki da na wasanni su kasance a kulle.
Duk a cikin bayanin nasa ya gargadi masu zuwa Sallah da su kasance sun sanya takunkumi suna bada tazara sannan da wanke hannu a koda yaushe.