Jami’an dake kula da hanyoyi sun sanar da turo ma’aikatan su guda dubu talatin da biyar, don kula da mutane wajan bikin babbar Sallah. Kamar yadda Jaridar pmPmne ta wallafa a shafinta
Bisi Kazeem, mai magana da yawun jami’an ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da hukumar yada labarai ta Najeriya.
Kazeem yace “akwai bukatar jami’ai da yawa don kula da hanyoyi da kuma jama’a a yayin gudanar da shagulgulan Sallah.”
KARANTA:- Yan majalisun Jahar Zamfara sun gayyaci mataimakin gwamna Mahadi Aliyu
Yace anyi hakane don inganta tsaron lafiyar mutane da hanyoyi lokacin bikin Sallah da bayan bikin Sallah.
Yace Jami’an za su cigaba da sintiri a kan Motoci suna sanya ido, don tabbatar da anyi bikin Sallah lami lafiya.
Yace hukumar ta samar da motocin jami’an guda dari bakwai da hamsin, da kuma motocin lafiya dari da ashirin, da manyan Motoci guda ashirin da biyar, da mashina guda dari biyu, inda za su fara aiki tun ranar sha shida ga wannan watan har zuwa ashirin da biyar na wannan watan.
Ya cigaba da cewa wannan dama al’adar hukumar ce na samar da ma’aikatanta a duk lokacin da za’a gudanar da wani biki a kasar nan.
Ya kuma jawo hankalin masu tuka Motoci da su hada Kai da Jami’an don gudun hukunci ga duk wanda ya karya doka.
A wani labarin
Kotu ta yanke musu hukunci shekara uku gidan kaso bayan kulle Yarinyar su a firiza
Wata kotun Majistret dake Sokoto ta yanke ma Emmanuel Bassey tare da matar sa Esther Emmanual hukunci shekara uku gidan kaso, biyo bayan kulle Yarinyar su mai kimanin shekaru 12 a cikin firiza har na tsawon wata takwas
Mai shari’ar Shuaibu Ahmad ya kuma sanya musu tarar dubu ashirin da biyar kan wannan mummunan aikin da sukayi.
Sannan ya kara saka musu tarar dubu dari biyu da saba’in da biyar.
Yace an kama ma’auratan dumu dumu da laifin, ya kuma Kara musu zaman gidan kaso na wata sha biyu da kuma tara naira dari, tun da farko dai an yake musu hukunci shekara uku gidan kaso.
Mai shari’ar yace za su fara zaman gidan kasonne nan take.
Ya Kuma baiwa Goodness Emmanuel da Happiness Emmanuel yaran Emmanuel Bassey beli akan 500,000 ko wannen su.
Jaridar Tvcnews ta ruwaito a watan May, 2021, cewar an sanya wata yarinya mai kimanin shekaru sha biyu a cikin firiza.
A dai lokacin makotansu suka kai rohoto ga jami’an Yan sanda aka kubutar da Yarinyar, sannan aka kama wadanda suka aikata laifin.