A ci gaba da rikicin APC da yake kaurewa, wanda masana harkokin siyasa suka ce yana da nasaba da zaben 2023, shugaban kasa Buhari ya ce yana goyon bayan Giadom ne domin bin umurnin kotu na ayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya ce shugaban kasa ya goyi bayan Giadom ne saboda bin umurnin kotu.
Bisa dukkan alamu wutar rikici na ci gaba da ruruwa a jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, sakamakon dakatar da shugaban ta Adams Oshiomhole da kuma samun halartaccen wanda zai jagoranci jam’iyyar.
A ranar Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin halartar taron shugabannin gudanarwar jam’iyyar da bangaren Victor Giadom ya kira, wanda kuma ya halarta a yau Alhamis, abin da ya batawa bangaren Bola Ahmed Tinubu rai, wadanda ke goyan bayan bangaren Prince Hilliard Eta dake cewa ba za su halarci taron ba, wanda kuma bayan taron suka ayyana taron a matsayin haramtacce.