Dan jaridar kasar Ghana mai bin diddigin labari, wato Anas Aremayau ya bayyana cewa; aikin jarida na bin diddigi da binciken kwakwaf, wani babban makami ne da zai taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Haka zalika Anas ya ce rahoton bincikar kwakwaf wani makami ne na yaki tare da shawo kan matsalolin cin hanci da rashawa a kasar nan, da ma nahiyar Afrika baki daya.
Anas Aremayaw ya bayyana hakan ne a yayin bude taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga masu aikin jarida na bincike da bin diddigi a nan gida Najeriya da kuma kasar Ghana da Malamai da dalibai masu nazari a jami’o’i da kwalejojin ilimi da kimiyya da fasaha wanda aka yi a harabar jami’ar Bayero dake Kano a ranar Alhamis.
Da yake jawabi kan yadda yake tattara bayanai wajen hada rahoton fallasa ko bankada masu cin hanci da rashawa, Anas ya ce akwai kalubale daban-daban da yake fuskanta, amma hakan bai kashe masa gwiwa ba, a don haka ya bukaci ‘yan jarida da dalibai masu nazari da su rinka bincikar kwakwaf wajen yin rahotannin kwarmata masu cin hanci da rashawa a cikin alumma.