Wakilinmu Mu’azzam Yakubu Sanka
A Martanin da Sarki Sunusi na II, ya aike da shi Bisa Tuhumar da Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa Reshen Jihar Kano, ke Masa a Dalilin Korafi da Wasu daga Cikin Masarautar suka Shigar Masarauta ta Kasa Kare Kanta.
In Baku Manta ba dai Hukumar Korafe-Korafe yaki da cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Karkashin Jagorancin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, ta aike ma da Sarki Takarda Kunshe da Wasu Tambayoyi Guda Sha Uku domin ya Baje Musu Bayani a Fili.
Inda Sarkin ya Kwararo Bayani a Rubuce Cikin Wata Takarda Mai Dauke da Sanya Hannun Sakataren Sarki Alh. Ali Abba Yusuf, Takardar da ta Musanta Kafatanin Zargin da ake ma Masarautar da cewa Ba Gaskiya ba ne.
Wanda Masarautar ta Ce lokacin da ta Hau Mulki Abin da ta Samu Naira Biliyan Daya da Miliyan Dari Tara, Wato 1.9 Billion Naira, amma abin Mamaki Maimakon Masarautar ta Kare Kanta a Tuhumomin da Hukumar ke Mata sai ta Buge da Tabbatar da Wasu daga Cikin Tuhumomin.
Misali Masarauta ta yi Bayani Kan Kudaden Zairga-zirgar Sarki a Jirgin Sama da Otel-Otel, da ya Rika Kwana ya Kashe Naira Biliyan daya da Miliyan Dari Hudu, da Kudin Katin Waya na Kamfanin Airtel, Naira Miliyan Ashirin da Tara.
Da Takardar ta ke Bayani sai taki cewa Uffan akan Batun Kamfanonin da Ba su da Rijista Wadanda aka yi Amfani da su Wajen Sutale Wadannan Kudade Wanda Akwai Asusu daya da Muka Samu na Wani Sunusi Tijjani, an Tunkuda Musu Kudi Sama da Naira Miliyan Dari da Biyar da Sunan Wani aiki Alhali aikin Bogi ne kawai.
Sannan ga Kuma Batun Maganar Wani Mai Suna Rufa’i Buhari, da aka Rika Amfani da shi Yana Canza Kudaden daga Naira Zuwa Dalar Amurka, shi da Wani Mutum da aka Dakile Cigaba da Binkicen sa da Cewa Wai Ya Mutu, Shi ma Takardar ta yi Gum a Kan su.
Sai Masarautar ta Mayar da Hankalinta wajen yin Bayanin Kudaden da ta Gada daga Marigayi Ado Bayero, Alhali Ita Hukumar Korafe-Korafe ba tana Magana Kan Kudin da Masaruta ta Gada ba ne tana Magana ne akan Kudin da aka yi Watandar su ta Katanga.
In Mai Adalci zai yi Duba da Idon Basira Meye Illar Cewa ana Tuhumar ka Wasu sun Kawo Korafi a kan ka Zo ka Kare Kanka sai ya zama Ala-ka-kai, kuma kai ta Zuge-zuge da Sunan Kai ba Mai Laifi ba ne, an ya Kuwa?
Za mu Cigaba.