Ministan Binin Tarayya Abuja Mallam Muhammad Bello ya yi amai ya lashe dangane da aikin hanya dake gudana a hanyar Apo zuwa Karshi.
Idan za a iya tunawa a ranar 17 ga watan Faburairun 2021 ne Ministan ya tabbatar da cewa ko tantama babu za a kammala aikin hanyar mai nisar kilomita 13.25 kafin fadiwar daminar bana.
To amma da yake wa manema labarai karin bayani jim kadan bayan fitowar su daga taron Majalisar Zartaswar Gwamnatin tarayya, Bello ya ce a yanzu haka fa labari ya sha banban da alkawarin da ya yi a baya.
Aikin hanyar kamar yadda Ministan ya ce an bayar da shi ne wa wani kamfani mai suna Kakatar Engineering Limited tun a shekarar 2011 sa’ilin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi alkawarin cewa gabannin fadiwar daminar bana za a kammala aikinhanyar a fara amfani da ita.
To sai dai sakamakon wannan koma baya da aka samu, Muyhammad ya dora alhakin jinkirin kan irin rashin nuna kwarewa gurin zanen hanyar inda aka yi shi daidai kan duwatsu.
Hanyar dai ta kulla abota da dukkanin hanyayi na cikin birnin tarayya abuja da kuma wasu kauyen ciki har da wasu yankuna a Jihar Nasarawa.