Kasar Birtaniya ta sanar da aniyarta ta haramta siyarda kwan wuta mai nau’in ruwan dorawa daga watan Satumbar wannan shekara inda za a maye gurbinsa da mai nau’in fari.
Wannan wani mataki ne na rage yawan dumamar yanayi da gurbataccen iska ke kawowa.
Mahukunta a kasar sun ce idan aka haramta saida kwan, lallai zai taimaka wajen rage tan sama miliyan daya na gurbataccen iska dake zuwa sakamakon kwan wutar, inda a lokaci guda kuma zai rage yawan zuke wuta da ake samu.
A shekara ta 2018 ne kasar ta fara siyarda kwan wuta mai nau’in fari wanda haskensa ya wuce misali, a wani mataki na bin Ka’idojin da Kungiyar tarayyar turai ta fitar.
A yanzu haka yan kasuwa dake dauke da kwayayyen a shagunansu na nufin cewa za su yi asara kenan, duba da wannan haramci.