Kimanin sa’o’i 48 da sace Bishop na cocin Jebba Diocese (Anglican Communion) Rt Reverend Adeyinka Aderogba, da matarsa, Oreofe da direban sa masu garkuwar sun sake su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Oyo Adewale Osifeso ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata a wata sanarwa daya fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar SEMA Ta Ziyar Ci Al’ummar Sokoto Wadanda Guguwar Iska Ta Lalatawa Gidaje
Sai dai Osifeso bai bayyana ko an biya wani kudin fansa ba kafin a samu sakin nasu.
Ya kuma danganta sakin nasu da cewa dinbin jami’an ‘yan sandan da aka sanya ayankin wadanda a cewarsa sun mamaye yankin baki daya kuma suka sa wadanda suka yi garkuwa da su su kubutar da mutanen.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin gurfanar da su a gaban kotu.”
Hakazalika wata majiya ta kusa da iyalan malamin da aka sace ta tabbatar da sakin, inda ta kara da cewa nan take aka kai wadanda lamarin ya shafa zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin kula da lafiyarsu.
Majiyar ta ce Bishop na Omu Aran Diocese, Rt. Rabaran Festus Sobanke da Babban Sakataren Cocin Najeriya Anglican Communion, Venerable Paul Dajur ya tabbatar fa sakin nasu.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa an yi garkuwa da Bishop Aderogba da matarsa da direban sa a hanyar Oyo-Ogbomoso a yammacin ranar Lahadin da ta gabata a hanyarsa ta zuwa Jebba bayan wani aiki na bishop a Yewa Diocese.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 domin su sake su.
Sai dai ba za a iya tabbatar da ko an biya wani kudin fansa daga cocin ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.