Jagoran Mayakan Neja Delta masu ɗaiɗaita bututan mai a yankin wato Alhaji Mujaheed Doku Asaru ya bukaci a tarayya da ta biya wa yan kungiyar Niger Delta Avengers bukatunsu.
Da yake zantawa da Jaridar Leadership a birnin Fatakwal, Asari ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban lasa Muhammadu Buhari ne ke kara harzuka mayakan ta hanyar bijiro da wasu tsare-tsare da za su kuntata wa al’ummar Niger Delta.
Ya ce tun bayan darewa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karagar mulki babu wani da aka zaba nagartacce a matsayin shugaban hukumar bunkasa yankin Niger Delta.
A cewar muddin ana bukatar zaman lafiya to tilas ne a yi wani abu a kan bukatun mayakan yankin.