Yayin da jami’an tsaro a faɗin kasar nan ke ci gaba da kokarin wanzar da tsaro a kasar, a hannu guda kuma an samu nasarar kubutar da biyu daga daliban makarantar sakandaren tarayya ta Birnin Yauri dake Jihar Kebbi.
Jami’an yan sandan sun yi nasarar kubutar da daliban ne a gandun dajin Dansadau dake Karamar Hukumar Marun Jihar Zamfara.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Zamfara CP Muhammad Shehu shi ya tabbatar da wannan nasara ga manema labarai a birnin Gusau a ranar Lahadi.
Ko d yake Kakakin Rundunar bai bayyana ko an biya kudin fansa ba gabannin kuɓutar da daliban, kazalika babu kididdigar adadin sauran ɗaliban da masu garkuwa da su din ke tsare da su ba.
Kimanin makonni shida kenan dai tun bayan sace daliban da wasu yan bindiga suka yi, adadin da har kawo yanzu ba a tantance ba.
Kazalika yayin harin na yan bindiga, jami’in dan sanda guda ya gamu da ajalinsa.
Lamuran matsalar tsaro a Nigeria dai na ci gaba ta’azzara, wadanda suka haɗa da Matsalar ta’addanci a shiyar arewa maso gabas, matsalar fashin daji da ya addabi arewa maso yammacin kasar da matsalar ballewar kasa da wasu marasa kunya ke yi a fadin kudancin kasar nan da suka hada da Inyamurai da Yarbawa.
Makarantu da dama a yankin Arewacin kasar nan suna ci gaba da fuskantar barazanar tsaro, inda baya ga jihar Kebbi akwai ɗalibai sama da 200 da aka yi garkuwa da su a a makarantar Islamiyya dake Jihar Neja.