Wata bokanya ta afka gidan wasu samari masu damfarar yanar gizo inda ta bukaci lallai sai sun raba kudaden da su ka damfaro da ita, LIB ta ruwaito.
A cewarta, tsafinta ya bayyana mata kudaden da su ka samu don haka ba za ta lamunce su ci kudin su kadai ba.
Bidiyon ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani da dama inda mutane su ka dinga mamakin karfin halinta.
An ji inda yake cewa tsafinta ya nuna mata kudaden da su ka samo a damfarar da su ka yi, don haka tazo da kanta ta amshi rabonta.
A bidiyon an ganta sanye da wata jar riga yayin da ta hakikance tana ta masifa inda take ganin kamar hakkin ta ne su ka lamushe su ka bar ta.
Kotu Ta Yankewa Masu Damfara Ta Yanar Gizo 66 Hukunci A Ibadan
Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta yankewa wasu masu damfara ta yanar gizo akalla sittin da shida (66) hukuncin dauri daban-daban da gidan yari.
Daily Post ta ruwaito cewa, Hukuncin daurin ya kai daga sati biyu, wata hudu da wata shida na yiwa al’umma hidima zuwa wata goma a gidan yari.
Hukuncin da aka yiwa masu damfarar yanar gizo ya biyo bayan kamasu ne da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta yi.
A baya dai hukumar EFCC ta kama wadanda ake zargin wadanda a halin yanzu aka yanke musu hukunci kan aika laifukan zamba daban-daban, .
Tun da farko dai hukumar EFCC shiyyar Ibadan ce ta gurfanar da wadanda ake tuhumar.
Masu damfarar ta yanar gizo kamar yadda Wilson Uwujaren, shugaban yada labarai da yada labarai na EFCC ya bayyana an gurfanar da su a gaban mai shari’a Olusola Adetujoye, Bayo Taiwo da Ladiran Akintola bisa wasu tuhume-tuhume da suka shafi laifukan zamba ta yanar gizo, tsakanin Litinin, 5 ga Satumba, 2022, da ranar Laraba 21 ga Satumba shekarar 2022.
Uwujaren, a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST a ranar Talata, ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da; Lawal Ismaila Adebola, Dazumi Azeez Jayeola, Morakinyo Abiodun Michael, Kehinde Samuel Olatunbosun, Yusuf Olawale Raji, Abass Akintayo Waliu, Kolawole Blessing Oluwafemi, Ajibade Habib Olakunle, Adedun Olajide Temidire, Dapo Ajayi Temitope Faith, Lami Patrick Olamide, Simoni Patrick Olamide, Lami Patrick Olamide Nurudeen, Obaloluwa Enoch Bolaji, Oladimeji Olamide Abdulrahman, Damilola Mubarak Muritala, Adedayo Wahab Abdullahi, Olotu Oluwadamilola Ayomikun, Aderibigbe Ibrahim Olamilekan, Sekoni Oluwatimilehin James, Dazumi Abdulrazak, Salami Ayo Wisdom da Ifeoluwa Joseph Olabiyi.