Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan Najeriya Laftanar Janar AbdulRahman Dambazau ya bayyana cewa Ƙungiyar Yarbawa Oduduwa da kuma Boko Haram Danjuma ne da Danjummai.
AbdulRahman Dambazau ya a fadi haka ne a yayin gabatar da wani Lakcha da ya gabatar gurin taron da aka shirya a Kwalejin Rundunar Sojin Yaki dake birnin tarayya Abuja.
Ya yi zargin cewa wadannan Kungiyoyi guda biyu an kafa su ne da aniyar kawo ruɗani wa kasar nan, wanda haka ne burin masu ɗaukar nauyin su.
Dambazau Kazalika ya ce bai kamata Jami’an Yan Sanda Su ma su naɗe hannu su zauna ba su bar aikin yaki da wadannan mutane kachokam ga jami’an soji ba.
Da yake Jawabi tun da farko, Hafsan Hafsoshin Tsaro Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya umarci dukkannin cibiyoyin tsaron sojin kasar nan da su tabbatar da gina jami’an sojin kan wani mizani da za su iya tunkarar duk wani kalubalen tsaro dake addabar kasar.