Rundunar sojin ƙasar nan ta yi nasarar mutane 94 da ƙungiyar Boko Haram ke riƙe da su a gabar Tabkin Chadi sun kuɓuta yayin da a ranar Alhamis aka miƙa su a hannun Gwamnatin Jihar Borno.
Rundunar haɗaka ta ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar a yankin Tabkin Chadi MNJTF, ita ce ke da alhakin wannan babbar nasarar.
Malam Isa Gusau, hadimi na musamman ga Gwamna Babagana Zulum kan harkokin sadarwa, shi ne ya labarta hakan cikin sanarwar da ya fitar a birnin Maiduguri.
Ya ce daga waɗanda abin ya shafa akwai maza 37 da mata 17 da kuma ƙananan yara da dakarun haɗin gwiwar suka ceto bayan sun yi ta artabu da ’yan ta’addan.
Ya ce kwamandan rundunar sojin, Manjo Janar Ibrahim Yusuf, shi ne ya miƙa wa gwamnatin jihar Borno mutanen, yayin da kwamishinan Shari’a, Kakashehu Lawan, ya karɓa a madadinta gwamnan jihar Babagana Umara Zulum.