Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kasance a kasar Kamaru a ranekun Talata da Laraba, inda ya gana da sama da ‘yan gudun hijira dubu 60 dake ‘kasar, wanda suka gujewa rikicin Boko Haram a jihar Borno.
Manufar wannan ziyarar shi ne domin bankado yadda za a tallafa musu da kuma duba yiwuwar komawarsa gida inda aka sake gina musu.
Majalisar dinkin duniya dake kula da ‘yan gudun hijira wanda suke kula da sansanin gudun hijirar Minawao inda gwamnan ya kai ziyara, a watan Mayun shekararnan sun tabbatar da cewa; akwai ‘yan gudun hijira dubu 86 ‘yan asalin jihar Borno a sansanin dake Borno.
Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, a sanarwar da ya fitar ya ce: Gwamna Zulum ya gana da ‘yan gudun hijirar, ya kuma tattauna da su akan yiwuwar gina gidaje a yankunan Banki, garin Bama, Pulka, Gwoza da Darajamal nan watanni biyu domin ganin an dawo da wadanda suke son dawowa gida.
Zulum ya jinjinawa gwamnatin Kamaru da al’ummar kasar bisa halin jin kan da suke nuna wa ‘yan Nijeriya daga Borno tun daga shekarar 2013 zuwa yau.