By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis ne tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi hasashen cewa nan bada dadewa ba Boko Haram za ta dauki yaran da basa zuwa makaranta aiki idan gwamnati ta kasa mayar dasu ajujuwa.
Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron bayar da horo ga matasan shugaban kasa da aka gudanar a cibiyar bunkasa matasa, a dakin karatu na Olusegun Obasanjo, dake Abeokuta, jihar Ogun.
Tsohon Shugaban kasar ya koka da yadda ake samun karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta, inda ya danganta matsalar tsaro da rashin samun ingantaccen ilimi.
Sannan ya yi nuni da cewa kimanin yara miliyan 14 ne daya kamata su kasance a makaranta suna kan tituna, yana mai cewa lamarin na iya kara tabarbara harkokin tsaron kasar.
Yace, “A halin da ake ciki a yau da muke da yara miliyan 14 daya kamata su kasance a makaranta wadanda ba su yi makaranta ba, shin akwai wanda ya kamata ya zama dan baka yace shekaru 10 ko 15 nan gaba, wadannan zasu kasance inda aka dauki aikin tsaftace Boko Haram.
“Don haka, idan kuka yi maganin Boko Haram da sanda a yau, nan da ‘yan shekaru, lamarin zai fi muni saboda muna maganar tsaro, zai fi muni.
Kazalika yace “To, idan muna maganar rashin tsaro, ta ina za mu fara? Idan ana maganar talauci, ta ina za mu fara? wannan ma Ilimi ne.
Tsohon shugaban kasar ya ci gaba da cewa hadin kan Najeriya shine abu mafi muhimmanci, yana mai jaddada cewa zai yi gwagwarmayar ganin an samu hadin kan Najeriya a tsawon rayuwarsa.Ya kara da cewa “Bani da nadamar fadan hadin kan Najeriya kuma idan har gobe za’a yi kuma ina da karfin yin hakan, zan yi abin da ya kamata in yi.”