A ranar Asabar ne ‘Yan tada kayar baya na Boko Haram suka kai hari a kananan hukumomi 3 dake jihar Borno, wannan ya biyo bayan wajabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a ranar Juma’a, inda yace ‘yan tada kayar bayan suna amfani da yanayin da ake ciki na annobar sarke numfashi, inda suke kai hare-hare.
‘Yan tada kayar bayan sun kai hari a kananan hukumomin da suka hada da; Gubio, Nganzai da kuma Monguno.
Sai dai Jami’an sojin shirin lafiya dole sun yi nasarar dakile harin da suka kai karamar hukumar Monguno.
Harin ya biyo bayan wanda suka kai kwanaki biyar da suka wuce, inda suka kai hari a kauyen Kolloram wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 81.
Sai dai ‘yan Boko Haram din sun sake kai hari a safiyar ranar Asabar a Dunga dake karamar hukumar Gubio a jihar Borno.
Har wa yau, a daidai lokacin da suka kai wannan hari na kauyen Dunga wani sashi na ‘yan tada kayar bayan sun kai hari a Usmanti dake karamar hukumar Nganzai kuma nan take suka kashe mutane 29.
Wani mazaunin yankin da ya gane wa idonsa, ya bayyanawa jaridar ‘THIS DAY’ cewa maharan sun kai farmakin ne da safiyar ranar Asabar kuma sun kashe mutane da dama, kafin jami’an tsaro su zo sun kashe mutane da dama daga baya kuma suka gudu.