Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a karamar hukumar Geidam dake jihar Yobe. Harin na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Nijeriya suka kashe shugabannin kungiyar Boko Haram/ISWAP a wani harin sama da runduna ta musamman ta Atisayen LAFIYA DOLE suka kai a Durbada dake jihar Borno.
Wadansu majiyoyi a Geidam sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun kai hari ta Kudancin kauyen Gumsa inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi. Wanda majiyarmu ta ce wannnan dalilin ya sanya mutane suka fara gudun ceton ransu sakamakon harin ya zo ne a daidai lokacin da al’umma suka fito sana’o’insu.
Al’ummar Geidam sun nuna damuwarsu, domin wannan shi ne karon farko da aka kai musu hari.
Hedikwatar tsarons sojojin Nijeriya ta hannun jami’in hulda da kafafen watsa labarai, Manjo Janar John Enenche a sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja ya ce sun tarwatsa wani gini na ‘yan Boko Haram din a wani hari da suka kai a ranar 17 ga watan Afrilu.