Kungiyar Boko Haram a ranar Alhamis ta bude wuta kan tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na dare.
Majiyarmu ta TheCable ta labarto cewa; bayanai daga wurin jami’an tsaro sun ce: ‘Yan Boko Haram din sun kai harin ne a daidai Konduga a yayin da gwamna Zulum ke dawowa daga wata tafiya da ya yi a karamar hukumar Bama na jihar.
Gwamna Zulum dai ya kai ziyara ne garuruwan Bayo, Kwaya Kusar, Askira Uba da Gwoza a wani yunkurinsa na kai ziyara dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar.
Bayanai sun ce; motar gwamnan da na wadansu Kwamishinoni sun tsallake rijiya da baya, amma motar karshe wacce take na sojoji ne ta sha ruwan alburusai. Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro na musamman dake cikin tawagar sun yi nasarar dakile harin a yayin da aka kawo shi.