Wakilin shiyyar Borno ta kudu a majalisar dattawa sanata Ali Ndume, ya bayyana yadda a rana ɗaya ’yan Boko Haram suka kashe mutum 93 a mahaifarsa ta garin Gwoza da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar ta Borno.
Ya ce 73 daga cikin dattawa 75 da aka kashe, an kai su wata mahauta aka yi musu yankan rago, baya ga wasu almajrai 20 da aka harbe su har lahira duk a rana ɗaya.
“Wata rana da sanyin safiya, mayaƙan Boko Haram suka ɗebi dattawa 75 daga garin namu, suka kai su abbatuwa a Gwoza kuma suka riƙa bi ɗaya bayan ɗaya suna musu yankan rago, sai dai mutum biyu sun tsira sakamakon jini da ya rufe su aka zata su ma matattu ne”, cewar Ndume.
“Mallam Durubu wanda maƙwabcina ne, mayaƙan Boko Haram sun harbe almajiransa 20 a rana ɗaya. Har yanzu zan iya tuna gidansu, ina iya tuna ranar da aka kwantar da su a ƙasa aka riƙa yi musu ruwan harsashi na bindiga.
Sanata Ndume ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Maiduguri, yayin wani zaman sauraron ra’ayoyin al’umma tare da masu ruwa da tsaki na jihar.
Kwamitin ayyuka na musamman na majalisar dattawa da kuma hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) su ne suka ɗauki nauyin shirya taron wanda aka gudanar domin yin bita a kan halin da yankin ke ciki a yanzu.
A yayin taron, Ndume ya ce a halin yanzu duk da kasancewarsa Sanata, ba ya da ikon shiga mahaifarsa ta Gwoza saboda rashin aminci da halin na rashin tsaro ya haifar.
Ya ce: “Ba na iya samun damar shiga dole sai dai a cikin tawaga ta rundunar sojoji”, inji Ndume wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa ta rundunar sojin ƙasar nan.