Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe shugaban kungiyar CAN na karamar hukumar Michika a jihar Adamawa.
A ranar Talata ne Mista Nicholas wanda da ne ga wanda aka kashe ya tabbatar wa BBC da mutuwar mahaifinsa, amma ya ce ba zai iya wani karin bayani ba don suna cikin alhini da makoki.
An dai yi garkuwa da shugaban kungiyar ne a farkon watan Janairun wannan shekara a wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a kauyensu.
Kwanaki kadan bayan da aka yi garkuwa da shi, an ga marigayin a wani bidiyo da ‘yan kungiyar Boko Haram din suka saki, inda aka ga malamin addinin yana rokon gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya ceto shi.