- Shugaban yana cikin ƙoshin lafiya
- Ya ƙaryata jita-jitar da ake ta yaɗawa
- Labarin ya ɗauki hankali matuƙa
Babban jigo a cikin jam’iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Asiwaju Bola Tinubu yayi dawowar bazata zuwa Najeriya ana tsakiyar yaɗa jita-jitar cewa ya mutu.
Dailytrust ta wallafa cewa masu yaɗa labarin mutuwar ta Bola Tinubu dai suna cewa wai ya mutu ne a sakamakon wata rashin lafiya da yake kan yi ma magani a ƙasar waje.
Labarin ya dauki hankali matuƙa, musamman ma dai a shafukan sada zumunta na zamani inda jama’a da dama sukai ta tofa albarkacin bakunan su.
Karanta wannan: Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin masana’antar iskar gas a jihar Rivers
Sai dai shugaban na jam’iyyar APC ya ƙaryata masu yaɗa labarin ta hanyar dawowar bazata zuwa gida Najeriya a tsakiyar cece-kucen.
A yammacin jiya Talata ne dai yan midiyar Bola Tinubu suka sanar da cewar mai gidan nasu ya dawo gida ta hanyar ɗora hotunan su a shafukan su na sada zumunta jim kaɗan bayan isowarsu Najeriya.
Ga wasu daga cikin hotunan dawowar ta Tinubu.
A wani labarin na daban kuma, shugaban EFCC, wato hukumar dake yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa na ƙasa wato Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa ana yawan yi masa barazana da rayuwar shi tun bayan da aka bashi shugabancin hukumar ta EFCC.
Bawa yace lallai mutanen da suke yaƙa bisa laifukan cin hanci suma suna maido da martani ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Buhari ma ya taɓa yin irin wannan furuci a shekarar 2016.
Shugaban EFCC yayi wannan jawabi ne yau talata a hira da shi da aka yi a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channels Tv.
Da aka tambaye shi ko yakan fuskanci barazana a yayin gudanar da ayyukan shi, sai ya kada baki yace: “Idan zaku iya tunawa naje birnin New York a satin da ya gabata. Wani babban mutum yake ce mun ya karɓi kiran waya daga wani mutum wanda binciken EFCC bai ma biyo ta kanshi ba, inda yake mishi iƙrarin cewa shi sai ya kashe shugaban EFCC wannan matashin yaron.
Comments 2