Alexander Dugin, masanin dabarun shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya rasa ‘yarsa, Darya Dugina.
Darya, ‘yar jarida wadda kamar mahaifinta ya goyi bayan mamaye Ukraine, ta mutu sakamakon fashewar wani abu bayan da na’urar ta tashi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Daraktoci 137 Sun Fadi Jarabawar Zama Shugabannin Makarantu
Motar Toyota Land Cruiser ta tashi ne da daddare a wata babbar hanya da ke kusa da kauyen Bolshie Vyzyomy mai tazarar kilomita 40 daga birnin Moscow.
Matashiyar mai shekaru 29 ta rasa yadda za ta yi a lokacin da take tuka mota da sauri sannan bom din ya ta tashi da ita zuwa wani wuri daga gefen hanya.
Gwamnatin Rasha ta zargi Ukraine da laifin mutuwar ta. Wani abokin dangin ya ce masanin kimiyyar siyasa ba shi ne aka shirya kaiwa harin ba.
Andrei Krasnov, shugaban kungiyar Russky Gorizent, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na TASS cewa, mai yiwuwa maharan sun biyo bayan mahaifin Darya ne.
“Kamar yadda na fahimta, makasudin shine Alexander kai tsaye, ko watakila duka biyu aka yi niyyar hallakawa,” in ji Krasnov.
Dugin, shugaban kungiyar Eurasian, ana daukarsa a matsayin “jagorancin ruhaniya” na Putin a yakin Ukraine. Rahotanni sun bayyana cewa ‘yar ta ari motarsa ne a cikin mintunan karshe.
Kwamitin bincike na Rasha ya fara bincike kan “kisan” da ya ce an yi “a cikin hadari”.
Shugaban jamhuriyar jama’ar ta Donetsk, Denis Pushilin ya zargi Kyiv da cewa shi ne ya shirya kai harin.
“‘Yan ta’adda na gwamnatin Ukraine, a kokarin kawar da Alexander Dugin, sun dauki ran diyarsa”, ya rubuta a kan Telegram.
Babban mai baiwa shugaban kasar Ukraine shawara Mykhailo Podolyak ya musanta zargin hannu a cikin mutuwar.
“Na tabbatar da cewa Ukraine ba ta da wata alaka da wannan saboda ba mu da wata kasa mai laifi, kamar Tarayyar Rasha kuma ba shakka ba ‘yan ta’adda ba,” Podolyak ya shaida wa gidan talabijin na Ukraine.
A wani labarin kuma Mummunar Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane 10, Ta Raba Sama Da 2000 Da Muhallan Su
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutane 10 a wata mummunar ambaliyar ruwa data afku sakamakon mamakon ruwan sama.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta rutsa da wasu kauyukan dake bakin koguna a karamar hukumar Girei, inda ta yi barna a gine-gine da filayen noma.