An harbe wani jami’in Dan sanda Mai mukamin Sufuritanda a jiya Alhamis har lahira, yayin da wasu biyu suka jikkata, bayan da masu baburan haya, suka yi bore a jihar Legas.
Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 5 na yammaci zuwa 6 yankin a Ajao Estate dake Isolo na garin Legas, yayin da jami’an rundunar yan sandan ke kokarin kwace babura Yan Okada.
Rahotanni sun nuna cewa, yan sandan sun kwace wasu Babura ne, saboda zargin su da keta dokokin zirga -zirga na jihar inda masu babura suka fusata Kuma suka farwa jami’an yan sandan.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Masu Babura sun kwace bindigan jami’in ne inda Kuma suka yi amfani da ta wurin kashe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobara ta tashi a Barikin Yan sanda dake Abuja
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, lamarin ya haifar da tashin hankali matuka a yankin.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Legas Adekunle Ajisebutu ya yi alkawarin yin bincike tare da sanar da wakilin Jaridar The Nation abun da ya faru, amma bai yi hakan ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Comments 1