Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Talata 30 ga watan Agusta, 2022 ta ba da umarnin sake gudanar da sabon zaben fidda gwani na dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Askira- Uba/Hawul na jihar Borno, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Alkalin kotun mai shari’a Jude Dagat, ya bayar da umarnin a sake gudanar da sabon zaben fidda gwani nan da kwanaki 14 domin a samu dan takara a jam’iyyar PDP saboda an soke zaben da aka yi a baya bisa rashin bin dokar zabe ta 2022 da Tsarin Mulki PDP.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Samu Gawarwakin DalibanJami’ar KWASU 2 A Dakin Kwanan Dalibai
Dr. Midala Usman Balami ne ya shigar da kara a gaban kotu yana kalubalantar sahihancin zaben fidda gwani da jam’iyyar PDP ta gudanar wanda aka ce INEC ce ke kula da shi a wani wuri daban da wanda kundin tsarin mulkin jam’iyya da kuma dokar INEC ta ayyana.
Mai shari’a Jude Dagat ya ba da umarnin cewa wadanda suka yi takara a baya kamar Dr. Midala Usman Balami da Alhaji Yerima da Engr Daniel Bassi da kuma Manjo Dika Nggada ne kawai za su shiga cikin zaben.
Da suke mayar da martani kan hukuncin, lauyoyin wadanda ke da’awar Gbenga Ayoola da Ibrahim H. Nggada sun bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar wa talakawa cewa akwai fata a cikin dimokuradiyya.
A wani labarin kuma Yajin Aikin ASUU: FG Ta Gayyaci NUC,VCs Zuwa Taro Na Musamman
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta aike da sammaci ga Pro-Chancellors, VCs, da Shuwagabannin majalisun jami’o’in tarayya zuwa wani taron tattaunawa na tilas da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga watan Satumba, 2022.
Hakan na kunshe ne a wata takardar da Hukumar kula da Jami’oin Najeriya (NUC) ta fitar a ranar 26 ga watan Agusta, 2022, amma ta samu zuwa yau Talata, 30 ga watan Agusta, 2022.