Bournemouth ta sayi dan wasan gaban Ghana Antoine Semenyo daga Bristol City kan kudi fan miliyan 9 (dala miliyan 11).
Ƙungiyar dai itace ke fafutuka a gasar Premier kuma ta sanar da wannan sauyi da ta samu a ranar Juma’ar nan.
KU KARANTA: Dan Takarar Mataimakin Gwamnan APC Ya Caccaki CBN
Semeyo ya amince da kwantiragin shekaru hudu da rabi, tare da Bournemouth, kuma tana da zabin tsawaita yarjejeniyar ta tsawon shekara guda.
Dan wasan mai shekaru 23, shi ne dan wasa na uku da Bournemouth ta dauko a kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu bayan mai tsaron gida Darren Randolph da dan wasan Burkina Faso Dango Ouattara.
Semenyo, wanda ya buga wa Ghana gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara, ya ci wa Bristol City kwallaye 21 a wasanni 125.
Kungiyar Cherries din tana mataki na 18 a gasar Premier bayan da ta samu daukaka daga gasar Championship a bara.
A wani labarin kuma: Fasinjoji Sun Makale Yayin Da Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Yi Hatsari
Kasa da mako guda bayan da jirgin kasan Itakpe-Warri ya kauce daga titin Kogi a Kogi, wani jirgin kuma a ranar Juma’a ya kauce daga hanya a babban birnin kasar nan Abuja.
Ma’aikatar jirgin kasa ta Abuja zuwa Kaduna, ta tattaro faruwar hatsarin a yammacin ranar Juma’ar Kubwa, inda daruruwan fasinjoji suka makale.