An garzaya da shugaban Brazil Jair Bolsonaro asibiti da sanyin safiyar Litinin domin jinyar wata matsalar toshewar hanji, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito.
Bolsonaro, mai shekaru 66, wanda ke kan mulki tun shekarar 2019, an kai shi asibitin Vila Nova Star da ke Sao Paulo.
Tashar talabijin ta Globo ta nuna hotunansa na sauka daga jirgin shugaban kasar da kafarsa tare da tawagarsa.
Likita Antonio Luiz Macedo, wanda ya yi wa Bolsonaro tiyata a wasu lokuta, ya shaida wa kafar yada labarai ta UOL cewa shugaban zai yi gwaje-gwaje da yawa don duba cikinsa.
Har yanzu dai hukumar yada labaran fadar shugaban kasar ko kuma asibitin ba su amsa bukatun neman bayanai da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya yi ba.
A watan Yuli, Bolsonaro ya shafe kwanaki hudu yana karbar magani saboda toshewar hanji.
Tun bayan harin wuka da aka kai masa a lokacin yakin neman zaben 2018, inda aka caka masa wuka a ciki, an yi masa tiyatar ciki akalla sau hudu.
Kimanin wata guda kafin a zabe shi a matsayin shugaban kasa, wani mutum da aka same shi da rangwame hanjaliyi ya caka masa wuka a wani gangamin yakin neman zabe.
AFP