Wata matashiya da har kawo yanzu ba a tantance wacece ba ta haukace jim kadan bayan da ta dirka daga wata mota a garin auchi na Jihar Delta.
Ko da yake ba a yi nasarar nadar bidiyon yadda ta sauka daga motar ba, amma wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda matashiyar ke ta gararamba kan titi bayan fitar ta daga motar.
Cewar wani wanda ya nadi bidiyon da kuma ya ce kada a bayyana ko shi wanene ya ce bayan da matashiyar ta sauka a motar sai ta zauna karkashin wani rumfa inda nan take ta tashi ta fara garma-garma.