Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya ta aike da wani saƙo kan budurwar da ta yi mata ƙwacen saurayi.
Budurwar dai ta sanya wani bidiyo ne a manhajar TikTok, inda ta aike da saƙon ga budurwar da saurayinta ya rabu da ita a dalilin ta. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Mata masu zanga-zanga sun dira hedikwatar INEC, suna neman wata bukata 1 kan Binani
Budurwar ta sanya wani tsohon bidiyo lokacin suna tare da saurayinta a cikin mota suna shan ƙauna kafin ya rabu da ita ya koma wajen wata daban.
Budurwar wacce ta girgiza matuƙa da abinda ya same ta, ta kuma sanya wasu bidiyoyinta tana sharɓar kuka bayan saurayin nata ya rabu da ita.
Daga nan sai cikin kuka ta roƙi sabuwar budurwar sa da ta kula da tsohon saurayin nata wanda ya rabu da ita a dalilinta.
Budurwar ta rubuta a ƙasan bidiyon cewa:
“Ki taimaka ki kulamin da shi, ya rabu dani ne saboda ke.”
Ku kalli bidiyon a nan
Bidiyon Wata Budurwa Mai Sharɓar Kuka Kan Rashin Saurayi Ya Yadu Sosai
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta shiga wani hali na ban tausayi saboda rashin saurayi
Wata matashiyar budurwa ta bayyana ɓacin ran da take ciki a dalilin rashin mashinshini.
Budurwar mai shekara 20 a duniya ta bayyana cewa kwata-kwata ba tada saurayi kuma abin yana ci mata tuwo a ƙwarya.