Wata budurwa ta maka wani mutum mai suna David a Kotu bayan da ya cece a ruwan iyo na makwabta yayin da take ƙoƙarin nitsewa.
Matashiyar ta ce dole ne mutumin ya girbi abinda ya shuka domin ba za ta yafe mishi ba.
Matashiyar Mai Suna Kim Wright mai shekara 23 ta ce Mista David ya yi amfani da damar da ya samu ne wajen tsamo ta ne ya aikata abinda ya ga dama da ita.
A yanzu haka ta iya yiwuwa a yi amfani da bidiyon yadda David ke matsa wa Matashiyar mama kana yaa sumbatar ta a matsayin shaidar cewa ya ci mata zarafi, duk cewa hakan na daga cikin dalilin farfadowar ta daga galabaita da take ciko.
Ko da yake Kim ta ce babu shakka ya yi kokari matuka, to amma a cewar kamata ya yi a ce ya bar wani ne ya cece ta ba shi ba, domin tsamin jikin shi ne ma ya sa ta farfado.
A yanzu haka ta ce dole ne a yi mata adalci domin yayi amfani da rauninta ne ya aikata baɗalar da ya ga dama.
” Da ya bar ni na mutu da ya gi sauki, yanzu gashi ya barni cikon tashin hankali, wani shashasha kawai ya zo ya ci mun zarafi wanda ban san ma menene ya kawo bakin ruwa ba” Cewar ta
Sai dai a ɓangaren David ya ce ya matuƙar kaduwa da wannan lamari na Matashiyar, kuma ya kara da cewa mudddin aka yanke mishi hukunci to lallai an nuna mishi rashin adalci karara.
“Na san cewa ni ma hankali na ba zai kwanta indai na barta ta mutu a lokacin, na san da cewa da ma akwai tsana da gaba da takw dauka ta da shi, amma ban taɓa tsammanin za ta gwammaci mutuwa ba a kan wai ni ne zan cece ta”
Daga hannu guda kuwa matashin da ya nadi bidiyon al’amarin mai suna Josh ya ce ya yi da na sanin daukar bidiyon, inda ya ce da ya san haka za ta faru da bai dauka ba.