Wata budurwa ƴar Najeriya wacce ta ke cikin farin ciki ta sanya wani bidiyo wanda ya nuna tulin kayan da saurayin ta ya biya a matsayin kuɗin aure.
Budurwa amfani da sunan @queenberry675 a TikTok ta kuma nuna yadda ɗaurin auren ta na gargajiya ya gudana, cewar rahoton Legit.ng
KU KARANTA KUMA: An Gurfanar Da Jami’in Sojan Bogi A Gaban Kuliya Bisa Wani Zargin Na Daban
A cikin bidiyon, budurwar ta tabbatar da cewa saurayin na ta lakadan ya biya kuɗin komai, sannan ba a biyo shi bashin ko sisi ba.
Bidiyon ya nuna kayayyakin da suka haɗa da doya, kayan sha, tufafi da sauran kayayyaki.
Haka kuma, an nuna lokacin da budurwar ta ke shiryawa saboda bikin. Ta cashe son ranta a lokacin da ake gudanar da bikin.
Mutane da yawa masu amfani da TikTik, sun yi ta taya murna sannan suka yaba wa saurayin na ta saboda namijin ƙoƙarin da yayi wajen haɗa kayayyakin.
Amma wasu sun buƙaci da ta nuna hoton mijin na ta, wanda gabaɗaya ba a nuna shi ba a cikin bidiyon, wanda yanzj haka har ya yaɗu sosai.
Ku kalli bidiyon a nan