Wani bidiyo wata budurwa da saurayinta daya yadu a kafofin sada zumunta ya tayar da kura, gospelarea.com ta rawaito.
A cikin bidiyon, an hangi wani matashi ɗan Najeriya da yake shirin angoncewa da budurwarsa a wani wurin cin abinci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Kebbi Bagudu Ya Amince Da Sakin Miliyan 100 Don Bunkasa Noman Kifi A Jihar
Saurayin ya nemi budurwar ta zama mahaifiyar ‘ya’yan da ba a haifa ba amma ita budurwar da ake zargin ta juya baya ta shararawa saurayin nata mari sannan ta tafi ta bar saurayin durkushe a kasa da zoben da ya saya na auren su a baya.
Da budurwar saurayin ta tafi, sai daya daga cikin mutanen da suka zo wurin cin abinci, ta zo ta taimaka masa tashi daga kasa.
Da suke mayar da martani ga faifan bidiyo da aka yi, da dama sun ce a cikin sa’o’i 24 masu kyau da Allah Ya ba mu, ya kamata mu fitar da sa’o’i 10 masu kyau don jin tsoron mata.
Wasu kuma sun yi addu’ar tare da taya saurayin da ake zarginsa jimamin abinda ya faru dashi.
A WANI LABARIN KUMA: Jam’iyyun siyasa ne ake so a yaƙa da Canja fasalin Naira – Deji Adeyanju
Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewa da siyasa, Deji Adeyanju, a ranar Talata, ya ce sake fasalin kudin Naira da babban bankin Najeriya, CBN ya yi, don ya shafi jam’iyyun siyasa na adawa ne ya sanya aka yi shi.
Adeyanju ya ce manufar CBN ta sa ‘yan adawa su rika zagayawa da kudi tare da zabukan da za a yi.