Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da wani uzuri na kin sanya hannu kan dokar gyara dokar zabe.
Wike ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Gidan Talabijin na Channels, a shirin Sunday Politics.
Ya kara da cewa sabanin ikirari na cewa Shugaban kasar ya ja baya saboda takun-saka a kan zaben fidda gwani na kai tsaye kamar yadda doka ta kunsa, babban batun shi ne watsa sakamakon ta hanyar intanet.
“Jam’iyya mai mulki a cikin makarkashiyarsu suna kokarin yaudarar ‘yan Najeriya cewa shigar da ‘yan takara kai tsaye a cikin kudirin gyaran dokar zabe shi ne matsalar da ya sa Shugaban kasa baya son sanya hannu ko kuma dalilin da ya sa ya ki sanya hannu.
“Babban batun shine watsawa, watsa sakamakon ta yanar gizo,” in ji Wike.
Gwamnan ya kara da cewa saboda akwai damar da za a yi wa wasu gyare-gyare a cikin kudirin dokar, shugaban kasar ba shi da hujjar da zai sa ba zai iya sanya hannu a kan kudirin ba, ya kuma yi kira da a sake duba sashin.
“Batun shine wannan, shugaban kasa ya rattaba hannu a kan kudirin dokar masana’antar man fetur kuma ya mayar da shi domin a yi wa dokar kwaskwarima.
“Idan shugaban kasa yana da kyakkyawar manufa ga kasar nan kuma kamar yadda ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin cewa yana son gudanar da zabe na gaskiya da adalci, to babu abin da zai hana shugaban kasar yin gyare-gyaren da aka yi masa sannan kuma ya nemi gyara dangane da tsarin gudanar da zabe kai tsaye. Na farko na jam’iyyun siyasa daban-daban,” Wike ya bayyana.
Ya kara da cewa, “Don haka idan wani ya ce maka abinitio, APC ta so ta goyi bayan watsa sakamakon zaben 2023 ta hanyar intanet, to lallai wannan mutumin ya zama dan wasa saboda na san cewa a 2018 da2019, dalilin da ya sa Shugaban kasa bai sanya hannu ba ne. saboda card reader. An gaya wa shugaban kasa, idan ka sanya hannu a kan hakan, zai kai ka ga gazawar zabe.”