Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci ƴan Diflomasiyya a Ƙasar, da kada su saka masu baki a Harkokin Siyasar Najeriya, a yayinda ake fuskantar Babban zaɓe na shekarar 2023.
Shugaban Ƙasar ya bada shawarar ne a Villa dake Abuja a lokacin da yake bada takarda ga Wakilan Jamhuriyar Czech Zdenek Krejci, Dana Itali Stephano De Leo, da Spaniya Juan Igancio Sell Sanz, gami da na Isra’ila Micheal Shual Freeman.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargaban mutuwar jami’an tsaro, yayin da yan binga suka harbi yan sanda da kami’ian kwastam a Enugu
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya taya su murna da shigowa Najeriya, ya buƙace su dasu tsaya a iya aikin su.
“Kuna fara aikin ku na Diflomasiyya a Najeriya, a lokacin da ake tsaka da siyasa, inda Najeriya ke fuskantar zaɓe a farkon shekarar 2023.