Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya aike da sako daga birnin Adis Ababa zuwa gida, inda ya ce yana da cikakkiyar masaniya kan wahalhalun da wasu manufofin gwamnati ke haifarwa, ya kuma sha alwashin daukar matakin da ya dace, yayin da ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, Daily Post ta rawaito.
Yayin da yake bayyana hakan a wata sanarwa, babban mataimaki na musamman ga Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana cewa:
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC Ta Musanta Kai Samame Gidan Tinubu
“A cikin sakon yakin neman zabe ga masu kada kuri’a, shugaban kasar ya yi kira na musamman ga “sarakunan gargajiya, malaman addini da iyayensu da su gargadi mabiyansu da kuma unguwannin su baki daya, kada su bari wasu su yi amfani da su wajen tayar da fitina.”
Sakon Buhari, kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar, takaitacce ne kamar haka:
“Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnati ta dauki kwararan matakan tsaro domin baiwa kowa damar fitowa ya kada kuri’arsa. Don haka ina kira ga kowa da kowa ya ba shi goyon bayan da ya dace.
“Yan uwana ‘yan Najeriya, ina so in yi amfani da wannan dama domin in sake gode muku da kuka zabe ni in zama shugaban ku a lokuta biyu.
“Ni ba dan takara ba ne a wannan zaben, amma jam’iyyata ta APC tana da dan takara a matsayin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Kamar yadda na ambata a baya, Tinubu mutum ne na gaskiya a Nijeriya mai son jama’a da ci gaban kasarmu.
“Ina kira gare ku da ku zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Shi mai dogara ne, kuma na yi imani zai gina kan nasarorin da muka samu.
“A karshe, ina da cikakkiyar masaniya kan irin wahalhalun da kuke fuskanta a halin yanzu sakamakon wasu manufofin Gwamnati da ke da nufin kawo ci gaba a kasa baki daya.
“Ina kira gare ku da ku kara hakuri yayin da muke daukar matakan da suka dace don saukaka wahalhalun. In sha Allahu za a samu haske a karshen ramin.”
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Shugaban APC Na Kasa Ya Shiga Ganawa Da Gwamboni 10
Gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da zai guna a ranar Asabar, shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu yana wata muhimmiyar ganawa da gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 2:35 na rana a dakin taro na kwamitin ayyuka na kasa NWC dake sakatariyar jam’iyyar, ya jawo hankalin gwamnonin Filato, Nasarawa, Neja, Kaduna da kuma Kogi.