Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya shaida wa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya yi tsammanin karin suka daga gwamnonin jam’iyyarsa ta APC. Daily Post ta rawaito.
Biyo bayan sabbin manufofinsa kan kudin Naira, da yanzu haka suka sanya yan Najeriya.
KU KARANTA: Austaraliya Zata Kashe Dala Biliyan 4.8 Ga Gasar Olympics Ta 2023
Shugaba Buhari, a jawabinsa na ranar Alhamis, ya umurci babban bankin Najeriya, CBN, da ya bar tsofaffin takardun kudi na Naira 200 su ci gaba da zagayawa cikin al’umma zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.
Tun bayan yada wannan labari ne wasu gwamnonin jam’iyyar APC suka shiga kakkausar suka ga matakin da shugaban kasar ya dauka, inda Gwamna Umar Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya caccaki Buhari kan kin bin umarnin kotun koli da kuma ci gaba da haramtawa tsofaffin takardun kudi na Naira.
A cikin wani faifan murya, an ruwaito Ganduje yana tambaya, “Ya kamata shugaba Buhari ya tuna cewa sau da dama yana kokarin tsayawa takarar shugaban kasa amma ya kasa yin hakan har sai da aka bujiro da wani tsari na daban.
Har ila yau, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai shima ya caccaki shugaban kasar kan matakin, inda ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden Naira.
A jawabinsa ga al’ummar jihar Kaduna, El-rufai ya bukace su da su tashi tsaye wajen tabbatar da dimokuradiyya, zaman lafiya da hadin kan kasa.
Kuma a nasa martanin, Shehu Sani, dan majalisar wakilai ta 8, mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Ya kamata shugaban kasa ya yi tsammanin karin suka daga gwamnonin jam’iyyarsa.
A wani labarin kuma: 2023: Wike ya koma APC a hukumance, yana yiwa Tinubu aiki – Kwamitin yakin neman zaɓen PDP
Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Rivers ta caccaki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da shiga jam’iyyar All Progressives Congress a jihar a hukumance.
Kwamitin yakin neman zaben Atiku/Okowa a jihar Ribas, ta bayyana cewa ziyarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya kai a gidan gwamnati ranar Laraba, bayan taron yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar APC a jihar, ya kawo karshen cece-kuce da ‘yan Najeriya ke yi,sannan Gwamna Wike ya musanta ra’ayinsa na siyasa.