Shugaban jam’iyyar ZLP (Zenith Labour Party) Mr Dan Nwanyawu, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tura da sunan Ibrahim Magu zuwa ga majalisar kasa domin tabbatar da shi a matsayin shugaban EFCC.
Nwanyawu ya yi wannan kiran ne a yayin da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce ayyukan alherin da Magu yake yi wajen yaki da rashawa, yana daya daga cikin dalilan da ya sanya ya yi wannan kiran.
Ya ce ya bi sahun ‘yan Nijeriya wajen kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya dauki matakin gaggawa wajen tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC ta hanyar aikawa majalisa sunansa domin tabbatarwa. Ya ce; yin hakan zai ba shi cikakkiyar dama wajen kama duk wadanda suka aikata ayyukan cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Nwanyawu ya ce wadansu rahotannin sirri na nuni da cewa wadansu na ta kai komo wajen ganin an sauya Magu din, ta hanyar sanya wani daban.
Shugaban Zenith Labour Party din, ayyukan wadannan masu son a sauya Magu din, zai kawo cikas ne kawai ga nasarar da EFCC ke samu a bangaren yaki da rashawa.