Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya sayar da hannun jarinsa a kamfanin Integrated Logistics Services Limited (INTELS), ya zargi gwamnatin Buhari da neman karya masa kamfani.
Kakakin jigon na jam’iyyar adawa ta PDP kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, Paul Ibe, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce an tilasta wa Atiku ɗaukar matakin ne saboda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari “ta matsu ta karya kamfanin” tun 2015.
Atiku ya kafa kamfanin na Intels tare da wani ɗan ƙasar Italiya mai suna Gabriele Volpi, wanda yake yi wa kamfanoni ayyuka musamman na man fetur da iskar gas.
“Atiku ya sha sayar da hannun jarinsa na kamfanin INTELS a baya amma abin ya yi ƙamari ne daga 2015 saboda burin wannan gwamnatin shi ne ta karya kamfanin da ke samar wa dubban ‘yan Nijeriya aiki kawai saboda siyasa,” in ji sanarwar.
“Ya sayar da hannun jarinsa na INTELS kuma ya mayar da kuɗinsa wasu ɓangarorin na tattalin arziki domin samun riba da samar da ayyukin yi. Ya kamata a riƙa bambanta siyasa da kasuwanci.”
A shekarar 2010 ne kamfanin ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da hukumar kula da gaɓar ruwan Nijeriya ta NPA, inda zai riƙa karɓar haraji a madadin hukumar game da wasu daga cikin ayyukanta.
Sai dai a 2017 Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce yarjejeniyar ta saɓa wa doka kuma gwamnati ta soke ta.
Kazalika, an sha zargin kamfanin da ƙin biyan haraji da kuma gaza biyan dala miliyan 48 ga gwamnatin Naijeriya.