Buhari

Buhari Na Yunkurin Rage Albashin Masu Mukaman Siyasa Don Biyan Karancin Albashi Ga Ma’aikata – Minista

A kokarinta na ganin ta iya biyan sabon karancin albashin N30,000 ga ma’aikatan Nijeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai yiwuwar za ta zaftare albashi da kuma alawus-alawus na masu rike da mukaman siyasa a duk fadin kasar.

Jaridar TheCables ta ruwaito ministan kwadago, Chris Ngige ne ya bayyana haka yayin da wakilan kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta NULGE suka kai masa ziyara a ofishinsa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

Ministan ya ce Kwamitinsu zai yi duba ga tsarin albashi na 12 da Nijeriya ke amfani da shi, sannan ya kara da cewa za su rage albashin duk wani mai rike da mukamin siyasa, ciki har da gwamnoni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *