Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da duk wata dama a mulkinsa wajan kawo karshen ta’addanci dake addabar kasar nan, sannan an kama duk wani mai yunkurin tada zaune tsaye don fuskantar hukunci. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wannan bayani ne lokacin da yake tattaunawa da Yan majalisu 469 wanda taron ya gudana a babban dakin taro dake Abuja, yace satar mutane, fashi da makami, ta’addanci da sauransu shine matsalar da muke fuskanta a wannan kasar.
Muna matukar damuwa kan yadda rashin tsaro ke haifar da tsaiko wajan habbaka tattalin arziqin kasar nan.
KARANTA:- DA DUMINSA: Majalisa ta ki amincewa da nadin Onochi a matsayin Shugabar INEC
A wajan taron shugaban Muhammadu Buhari ya yabawa Yan majalisu na tara kan irin rawar da suke takawa wajan tabbatar da aikinsu da kuma cigaban kasa da suke kawowa.
Ya kuma yabama sauran Yan majalisu marasa rinjaye kan irin hadin kai da suke badawa don ganin an gina kasar nan.
A cikin jawabin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lissafo wadansu ayyuka wanda Yan majalisu suka kammala.
Ya kuma yaba musu sosai karkashin jagorancin Shugaban Yan majalisu Ahmad Lawan da kuma Femi Gbajabiamila don sadaukar da kansu wajan kawo sauyi a kasar nan.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Yan majalisu sun shigo Ofishin cikin wani yanayi amman duk da haka suna taka muhimman rawa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace zai cigaba da hada kai da sauran Yan majalisu da Sanatoci don cigaba Kasar nan.
A wani labarin
RIKICIN JAM’IYYA: Batun dakatar da Rochas Okorocha karya ne, cewar APC
Shugaban Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ya misanta zancen da ake yadawa na korar Rochas Okorocha, yace karya ne ba gaskiya bane.
A ranar Talata ne Sakataren jam’iyyar APC na Kasa yace mayaudara ne sukayi amfani da siginato na jam’iyyar wanda aka baiwa hukumar INEC suka sanya a takardar bogi ta sallamar Rochas Okorocha.
Kamar yadda bayanin nasa yake “A halin yanzu jam’iyyar APC ba ta da wani “kwaniti na kasa” kamar yadda aka bayyana a cikin wasikar, sai dai kawai kiya teka CESPC ne wadanda ke rike da jam’iyyar, wanda suke kula da jam’iyyar.
Muna Kira ga sauran masu kishin Al’ummar wasu mayaudara nayin iya bakin kokarin su wajan haifar da tarzoma a cikin jam’iyyar ta hanyar yada labaran bogi, muna Kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su rinka karbar bayanai ta ingantattun kafafen watsa labaran mu.
Muna Kuma Kira ga sauran jama’a da su dauki dakatar korar Rochas Okorocha a matsayin karya ba gaskiya ba.