Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fahimci siyasa ba.
A lokacin da yake jawabi ga wakilai da shugabannin jam’iyyar a Katsina a ranar Lahadi, Mohammed ya ce Buhari ya kasa cika abin da ake tsammani saboda yana kewaye da mutane mayaudara.
Ziyarar dai na daga cikin ganawarsa da ‘yan jam’iyyar gabanin gudanar da zaben fidda gwani.
“Al’ummar jihar Katsina sun yi manyan ayyuka domin ci gaban kasar nan, misali shi ne abin da marigayi Shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya yi wa Nijeriya, Allah Ya jikansa da rahama.
“Amma abin takaici, danka, mahaifinmu, shugaban kasa na yanzu, mutane marasa gaskiya ne, makaryata wadanda ya dauka mutane ne masu gaskiya, saboda shi soja ne, bai san mutane ko siyasa ba.
“Mun san kowa da kowa, na kirki da na banza, dole ne mu gyara wannan mummunan ra’ayi na cewa mu duka mutane miyagu ne, dole ne mu tabbatar da makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu, kuma muna bukatar masu karewa irina,” in ji shi.
Mohammed ya ce idan aka ba shi dama, zai yi amfani da gogewar da ya tattara a matsayin dan jarida, ma’aikacin gwamnati, dan siyasa da kuma ma’aikacin gudanarwa wanda ya rike mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja na tsawon shekaru shida kuma gwamnan jihar Bauchi, domin mayar da kasar nan kan turba.
Ya ce idan ya zama shugaban kasa a 2023, zai magance matsalolin fatara, yunwa, rashin tsaro da kuma dawo da mutuntawa da martabar ‘yan kasa a ciki da wajen kasar nan.
“Wannan batu na ‘yan fashi ya zama tamkar wani shiri da hatta sojojin da ke yaki sun zama marasa kima a yakin, ba a ba su kayan aikin da ake bukata domin tunkarar makiya. Dole ne mu zabi mutanen da za su iya ceto lamarin,” ya kara da cewa.