Ƙungiyar ƴan majalisa marassa rinjaye na Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ƙalubalanci jawabin da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar, a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kashi na 76.
A cikin wani jawabi da shugaban Shugaban Marassa rinjaye Ndudi Elumelu ya sanyawa hannu, yace ƙungiyar data haɗa da yan majalisar PDP tayi dubi akan jawabin da shugaban ƙasa ya gabatar.
Sanarwar tace jawabin daya gabatar ya saɓa da munanan halin da Gwamnatin sa take ciki, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yiwa sama da mutane Miliyan 4.6 rigakafin Covid-19 a Nigeria — inji Gwamnatin Tarayya
Ƙungiyar tace a ƙarƙashin gwamnatin sa, an samu matsin tattalin arziki da matsalar tsaro, gami da walwalar jama’a da suke cigaba da tunkarar gwamnatin sa.
“Ƙungiyar mu ta tsaya akan cewa jawabin da shugaban ƙasa Buhari ya gabatar koma baya ne ga ƙasar, na yadda bai gayawa shuwagabannin duniya halin da ƙasar ke ciki, na take haƙƙin bil’adama, da cin hanci, da rashin iya mulki a ƙarƙashin gwamnatin sa, da kawo wahalar rayuwa, da matsalar tsaro gami da hana wasu ɓangarori kawo taimako a ƙasar,” inji shi.
Sanarwar ta kuma ƙara dacewa, abin kokawa ne rahoton shugaba Buhari a Majalisar Ɗinkin Duniya cewa a halin yanzu an karya lagon ƴan ta’adda a Nigeria.
“Alhali a zahiri, ƴan ta’adda sun yi karfi a ƙarƙashin gwamnatin sa, inda suke kai hari ga sojoji, gami da yin garkuwa da mutane da sauran su ba ƙaƙƙautawa.”
“A matsayin mu na wakilan al’umma, munji damuwa akan jawabin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari na yadda baiyi magana, akan garkuwa da mutane gami da sace ɗalibai ƴan makaranta a Nigeria.
Haka zalika, jawaban basu nuna cewa an kulle makarantu ba, wanda hakan zai haifar da koma baya ga ilmi a sassa da dama na ƙasar, inda ƴan ta’adda suka haifar da rashin kwanciyar hankali, kuma bai nuna jaje ga waɗanda harin ya shafa ba” inji jawabin